Kamfanin dillancin labaran kasa
da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarta
maku cewa: sojojin yahudawan sahyoniya suna ci gaba da yin kisan kiyashi
a zirin Gaza a yau din da ake cika rana ta 311 a jere ta hanyar kai hare-hare
ta sama da harsasai da kashe fararen hula a cikin wani mummunan yanayi na jin
kai sakamakon hare-hare da sojojin suke ci gaba da kaiwa Mazauna wannan yanki
wanda su kaiwa kawanya.
Dangane da haka ne tashar Al-Mayadeen ta bayar da rahoton cewa, jirage marasa matuki na kunar bakin wake na gwamnatin sahyoniyawan sun yi ruwan bama-bamai a wani gida da ke unguwar "Absan Al-Jadedeh" da ke gabashin Khan Yunus.
Wakilin Al-Mayadeen a zirin Gaza ya sanar da cewa: An mika shahidai 12 zuwa asibitin "Nasser" sakamakon harin bam da yahudawan suka kai a Khan Yunus.
A cewar wani rahoton, Falasdinawa 2 ne kuma suka yi shahada sakamakon harin bam da aka kai a kofar shiga sansanin Al-Nusirat da ke tsakiyar zirin Gaza.
Sannan a ci gaba da aikata laifukan na yau jiragen yakin Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a wani gida da ke unguwar Al-Sheikh Rizwan da ke arewacin zirin Gaza.